Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: majalisar dokokin kasar Iraqi ta dage tattaunawa da nazari tare da kada kuri’a da amincewa da dokar Hashdush Sha’abi zuwa wani zama na gaba na majalisar saboda takaddamar siyasar cikin gida da kuma matsin lamba daga kasashen duniya. Wannan yunkuri ya zo ne a daidai lokacin da kwamitin tsaro na majalisar dokokin Iraki ya sanar a baya cewa an shirya daftarin karshe na dokar don kada kuri'a.
Neman Tattauna Dokar A Hukumance A Zauren Majalissar A Bayyane
Shugaban Kwamitin Tsaro da Kariya na Majalisar Dokokin Iraki Karim Aliwi al-Hamidawi, ya sanar a jiya cewa, an shirya dokar Hashdush Sha’abi bayan karantawa ta biyu, kuma an yi la'akari da duk wani tsokaci da shawarwari. Mun aika da wannan doka ga Majalisar Shugaban kasa don shigar da su cikin ajanda.
Rikicin Cikin Gida Da Matsin Lambar Kasa Da Kasa Ya Kawo Cikas Ga Amincew Da Dokar.
Sai dai wata majiyar 'yan majalisar dokokin Iraki ta shaida wa Erem News cewa: Majalisar shugabancin majalisar ta yanke shawarar jingine nazarin wannan doka saboda rarrabuwar kawuna tsakanin bangarorin siyasa da kuma tsoma bakin kasashen yammacin duniya musamman Amurka.
A cewar wannan majiyar, akwai fargabar cewa amincewa da wannan doka zai halasta kungiyoyin da ba na gwamnati ba, wadanda kasashen yammacin duniya ke kallonsu a matsayin kalubale ga zaman lafiyar al'umma da bin doka da oda a Iraki.
Abubuwan Da Rikicin Tsaro Na Kwanan Nan Ya Haifar
Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa aka dage dokar Hashdush Sha’abi, shi ne irin abubuwan da suka faru na tsaro a yankin Saydiya na Bagadaza. A cewar majiyoyin, rikicin da ya barke a cikin ginin ma'aikatar noma, ya sake bayyana irin tasirin da kungiyoyin da ke dauke da makamai ke da shi a cikin hukumomin gwamnatin Iraki, tare da nuna damuwa kan yadda gwamnatin kasar ke da ikon sarrafa makamai da kungiyoyi masu dauke da makamai.
Matsayin Gwamnatin Iraqi
Firaministan Iraki Mohammed Shi'a al-Sudani ya sha nanata cewa yanke shawara kan yaki da zaman lafiya ya rataya a wuyan gwamnati ne, kuma idan aka yi la'akari da yanayin tsaro a Iraki, babu wata kungiya da ke da hujjar daukar makamai.
A wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press a makon da ya gabata, ya ce yadda gwamnati ta ke da hannu wajen samar da makamai yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro, kuma wani bangare ne na shirin gwamnatin Irakin.
Dakarun Hashdush Sha’abi: Cibiya Ce Ta Hukuma Ko Ƙungiya Ce Mai Dauke Da Makamai?
Duk da cewa firaministan kasar Iraki ya tabbatar da cewa Cibiyar Hashdush Sha’abi wata cibiya ce a hukumance, kuma wani bangare ne na sojojin kasar, amma har yanzu takaddama kan batun rawar da cibiyar ke takawa, da ikonta, da kuma alakarta ta siyasa, na daga cikin batutuwan da suka fi fuskantar kalubale a Iraki.
Your Comment